An gabatar da kasafin N4.6 tiriliyan a Nigeria

Image caption Ngozi Okonjo-Iweala.

Ministar kudin Nigeria, Ngozi Okonjo-Iweala ta gabatar da kudirin kasafin kudi na Naira tiriliyan 4.6 ga majalisun dokokin kasar a madadin shugaba Goodluck Jonathan.

Tun bayan komawar Nigeria tsarin dimokradiyya a 1999, shugabannin kasar ne ke gabatar da kudirin kasafin kudi ga majalisun, in ban da lokacin da marigayi shugaba Umaru Musa 'Yar'adua ke jiyya a kasar Saudiyya.

Koda yake fadar shugaban kasar ba ta baiyana dalilin tura wakilcin ba, manazarta na ganin hakan ya biyo bayan sabanin siyasar da ke faruwa ne tsakaninsa da musamman 'yan majalisar wakilai ta kasar.

Madam Okonjo-Iweala ta mika kundin kudirin kudin ne ga majalisar dattawa da ta wakilai ta kasar ba tare da karanta abinda kundin ya kunsa ba.

Majalisun biyu za su tattauna tanade-tanaden kasafin kudin domin gyara da amincewa bayan dawowa daga hutun Kirsimeti da sabuwar shekara.