Yaki na yaduwa a Sudan ta Kudu

Image caption Sudan ta Kudu na fuskantar barazanar yakin basasa.

Yaki na ci gaba da yaduwa a Sudan ta Kudu tsakanin sojoji da 'yan tawayen da ke goyon bayan gudajjen tsohon mataimakin shugaban kasa Riek Machar.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce masu aikin fetur a garin Bentiu dake arewacin kasar sun nemi mafaka a sansanin majalisar.

Rundunar sojin kasar ta ce an kwace garin Bor da ke kudancin kasar daga karkashin ikonta bayan da aka yi kazamin fada.

Rikicin da aka fara a Juba, babban birnin kasar ya hallaka mutane 500 tare da haddasa fargabar yakin basasa.

Idan an jima a yau, wata tawagar jami'an Afrika za su isa Juba domin tattaunawa tsakanin bangarorin biyu.