Gwamnatin Syria na sace farar hula

Image caption Dubunnan mutane ne ke bacewa a rikicin Syria.

Masu binciken hakkin bil'adama na Majalisar Dinkin Duniya sun ce dakarun gwamnatin Syria na sace fararen hula sannan su musanata masaniya game da su, a wani shiri da zai iya zama laifin keta zarafin bil'adama.

Rahoton majalisar ya ce dubunnan mutane ne suka bata, kuma mafi yawansu ba'a kara ganinsu ba.

Rahoton ya ce wadanda suka fara bacewar wadanda suka shiga zanga-zangar adawa da gwamnati ne, amma yanzu har da likitocin da ke kula da 'yan tawayen da suka ji rauni ake sace wa.

Masu binciken sun ce wadanda suke bin kadin abinda ya faru ga wadanda suka bace su ma ana sace su.