'Yan kwadago sun balle daga jam'iyyar ANC

Image caption Jam'iyyar ANC ta yi fice wurin yaki da wariyar launin fata a Afrika ta kudu amma yanzu tana cikin rikici.

Babbar kungiyar kwadagon Afrika ta Kudu ta ce ta daina goyon bayan jam'iyyar ANC mai mulkin kasar.

Kungiyar ma'aikatan karafa ta Afrika ta Kudu, wacce ke da wakilai fiye da dubu 300, ta bayyana haka ne a taronta na musamman.

Jam'iyyar ANC ta mamaye siyasar kasar ne bayan da ta kulla kawance da hadakar kungiyoyin kwadagon kasar da kuma jam'iyyar gurguzu.

ANC ce dai ta lashe duk zabubbukan da aka yi a kasar tun 1994, amma ta sha suka a baya bayan nan bisa batun rashin aikin yi da cin hanci da rashawa.