An yi musayar wuta a Bama ta jihar Borno

  • 20 Disamba 2013
Image caption Ana zargin 'yan Boko Haram ne suka kai harin.

Wasu 'yan bindiga sun kai farmaki a barikin sojin kasa na Nigeria dake garin Bama a jihar Borno, inda su ka yi musayar wuta da jami'an tsaro.

Rahotanni sun ce sojin saman kasar sun yi amfani da jiragen sama na yaki wajan mayar da martani ga gungun mutanen da ake zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne.

Harin da aka fara kaiwa tun karfe ukun daren Juma'a ya janyo artabu tsakanin sojojin Najeriya da kuma gungun mutane dauke da makamai da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne.

Maharan sun kai harin ne a barikin soji na 202 dake Bama wanda yake da nisan kilomita 40 daga birnin Maiduguri a Jihar Borno.

Kawo yanzu babu cikakken bayani kan asarar rayuka da dukiyoyi amma wata majiya na cewa an kashe mata da yara a barikin.

Wannan harin na zuwa ne kusan makwanni uku bayan da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai wani hari na ba zata kan barikin sojin kasa da kuma wani ofishin sojin sama na birnin Maiduguri.

Kakakin rundunar sojin Najeriya dake kokarin dakile hare-haren 'yan kungiyar Boko Haram a Jihar Borno, Kanar Muhammad Dole ya tabbar da afkuwar lamarin amma bai bada karin bayani ba.

Karin bayani