Blackberry ya yi asarar $4.4 biliyan

Image caption BlackBerry na karkata akala daga wayoyi zuwa manhajar salula.

Kamfanin BlackBerry mai samar da wayar komai da ruwanka ya ce ya tafka asarar dala biliyan hudu da miliyan 400 tsakanin watannin Yuli da Satumban bana.

Kamfanin ya ce adadin wayoyin da ya sayar a lokacin bai kai rabin abin da ya sayar a daidai wannan lokacin a bara ba.

Wannan dai shi ne sakamako na farko da shugaban rikon kwarya na kamfanin John Chen ya fitar.

Ya ce kamfanin "na nan daram" sai dai yanzu yafi mai da hankali ne kan cinikin manhajar wayoyi maimakon wayoyin kansu.