Matsala a kasafin kudin Najeriya

Ministar kudin Najeriya
Image caption Masana na ganin da wuya a iya aiwatar da kasafin kudin ba tare da wasu matsaloli ba.

Wasu masana tattalin arziki a Najeriya sun bayyana cewa da wuya kasafin kudin da gwamnati ta gabatar a gaban majalisun dokoki na kasa ya yi aiki.

Ranar Alhamis ne dai ministar kudin kasar,Dr Ngozi Okonjo-Iweala, ta gabatar wa majalisar wakilai da ta dattijai daftarin kasafin kudin na naira kusan tiriliyan biyar.

An dai ware sama da naira tiriliyan biyu ne, wato kashi 73 cikin dari, na kasafin kudin don ayyukan yau da kullum.

Wani mai sharhi Malam Yusha'u Aliyu na ganin kasafin kudin na da gibi da dama.