India na neman kotu ta halatta luwadi

Image caption 'Yan luwadi da madigo na zanga-zangar kare hakkinsu a India.

Gwamnatin India ta bukaci kotun kolin kasar da ta sake nazari kan hukuncin da ta yanke na tabbatar da wata tsohuwar doka da ta haramta luwadi da madigo.

Gwamnatin ta nemi kotun ta sake duba hukuncin da ta yanke a farkon watan nan ne, inda ta ce dokar ta sabawa akidar adalci tsakanin al'umma.

Daruruwan masu kare hakkin 'yan luwadi da madigo ne su ka gudanar da zanga-zanga game da hukuncin da ya nuna za'a iya daure masu auren jinsinsu.

A baya dai kotun kolin ta ce aikin majalisar dokoki ne ta sauya dokar.