Kiyasin yawan 'Yan Sunna da 'Yan Shi'a

Akwai musulmai fiye da biliyan daya da rabi a duniya kuma kusan kashi ashirin cikin dari suna zaune ne a Gabas ta Tsakiya da kuma Arewacin Afrika.

Musulmai sun kasu kashi-kashi wasu na bin akidar Sunna wasu kuma 'yan shi'a ne.

Babu cikakkun alkaluma kan adadin yawan Musulmai a duniya da ke bin mazhabobi daban-daban.

Wannan taswirar na nuna kiyasin yawan 'yan Sunna da 'yan Shi'a.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Galibin Musulmai 'yan Sunna ne inda a wasu wuraren sun kai kashi 85 zuwa 90 cikin 100.

Kasashen da suka fi yawan 'yan Sunna a Gabas ta Tsakiya su ne Masar da Jordan da kuma Saudi Arabiya inda su ka kai kashi 90 cikin 100.

'Yan shi'a ba su wuce kashe 10 cikin 100 ba amma kuma adadinsu ya kai miliyan 154 zuwa 200, kamar yadda rahoton Pew na shekara ta 2009 ya nuna.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Iran ce ta fi kowacce kasa yawan 'yan Shi'a inda mutane fiye da miliyan 66 a kasar watau kusan kashi 90 cikin 100 na al'ummar kasar 'yan shi'a ne.

'Yan Shi'a na da rinjaye a kasashen Iraki da Bahrain. Sannan kuma akwai 'yan Shi'a a Kuwait da Yemen da Lebanon da Qatar da Syria da Saudiyya da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa.

A kasashen da akwai dinbim 'yan Shi'a, ana yawan nuna bambamci da kuma samun matalauta.