Ana ci gaba da arangama a Sudan ta Kudu

Image caption Rikicin kabilanci ya yamutse a Sudan ta Kudu.

Ana samun rahotannin ci gaba da arangama a Sudan ta Kudu, wacce shugaba Obama ya yi gargadin ta na daf da fadawa yakin basasa.

An kai dakarun gwamnati zuwa yankin arewacin kasar mai arzikin man fetur, inda Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana kazamin fada tsakanin kabilun Nuer da Dinka.

Matasan Nuer sun kace sojojin kiyaye zaman lafiya na majalisar guda biyu a Akobo ranar Alhamis.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce yankin na cikin rudani, yayin da dubunnan mutane ke tserewa.