Dalilin rikicin Sudan ta Kudu

Image caption Yaki ya rutsa da dubunnan mutane a Sudan ta Kudu.

Sudan ta Kudu na fuskantar kalubale mafi girma a tarihinta tun bayan samun 'yancin kai.

Abin da ya fara a matsayin "yunkurin juyin mulki" ga gwamnatin shugaba Salva Kiir - koda yake wanda ake zargi ya musanta hakan - ya sauya zuwa wani abu da ke barazana ga kasar baki daya.

Sojojin kasar sun ce dakarun da ake ganin suna karkashin Janar Peter Gadet sun kwace Bor, babban birnin jihar Jonglei.

Sai dai kuma inda lamarin ya kara baci, shi ne yadda fadan ke iza wutar rikici tsakanin kabilun kasar da ba sa ga-maciji da junansu.

Abin tsoro

Image caption Salva Kiir ya zargi mataimakinsa da juyin mulki.

Masani kan harkokin Sudan ta Kudu, Douglas H Johnson na ganin abubuwa biyu ne suka haddasa rikicin.

Sabani cikin jam'iyyar SPLM mai mulkin kasar da batun shigar da 'yan bindigar da ke alaka da gwamnatin Sudan cikin rundunar sojin kasa.

Mr Johnson ya ce: "Hankalin wadannan sojojin ba a kwance yake ba."

Daya daga cikinsu Janar Gadet, ya dauki makamai bayan da rahotannin daga Juba suka ce ana ta kashe 'yan kabilarsu ta Nuer.

Mr Machar da Janar Gadet 'yan kabilar Nuer ne, amma a baya kansu ba hade yake ba.

Kawo yanzu babu tabbacin tare su ke wannan tawayen.

Duk da haka, gwamnatin Kudan ta Kudu na ganin bakinsu daya.

Wannan lamari ne mai ban tsoro.

Kwan-da-shirin-yaki

Image caption Riek Machar ya musanta yunkurin juyin mulki.

Janar Gadet jajirtaccen mayaki ne wanda ya sha yi wa jam'iyyar SPLM tawaye.

Wani kwararre kan yankin Sudan, John Young, ya kira shi da "kwan-da-shirin-yaki" saboda kullum ya na bakin fama.

Luka Biong, wani tsohon ministan SPLM da yanzu yake jami'ar Harvard ya ce: "Ana kallon Gadet a matsayin mai biyayya ga jagorancin Riek Machar da Taban Deng, tsohon gwamnan jihar Unity, wanda shi ma gwamnatin ke nemansa ruwa a jallo.

Sai dai wannan hadakar ta karfin soji da siyasa na iya mummunar barazana ga gwamnati, fiye da tawayen da Janar Gadet ya yi a baya ko kuma wadanda wasu sojojin irinsu Bapiny Montuil da George Athor su ka yi.

A shekarar 1991, lokacin da Mr Machar ya balle ya kaba ta sa kungiyar 'yan tawayen dakarun kabilar Nuer dake tare da shi sun kashe akalla Dinka 2,000a Bor.

A yayin da sojojin Nuer na Janar Gadet ke kai hari Bor, 'yan Dinka da dama na fargabar tarihi zai maimaita kansa.

Sarkakkiyar siyasa

Image caption Akwai jikakkiya tsakanin kabilun Dinka da Nuer.

Shugaba Kiir da Mr Machar za su fuskanci matsi kan sasantawa.

Sai dai, ba mamaki idan hakan bai faru ba, ko kuma bai kawo karshen yakin ba.

Mr Biong na fargabar cewa Janar Gadet zai iya hadewa da jagoran 'yan tawayen kabilar Murle, David Yau Yau, wanda shi ma ya ke jihar Jonglei.

Idan ya yi hakan, to lamari ya sauya ke nan domin ya na daga cikin dakarun sojin da ke yaki da David Yau Yau.

Duk da haka, a cikin sarkakkiyar siyasar Sudan ta Kudu, wannan ba abin mamaki ba ne tun da dukkansu na da dangantaka da gwamnatin Khartoum.

Haka kuma akwai bukatar sa ido kan jihohin Unity da Upper Nile.

Akwai dubunnan matasa a jihohin da ma yankin Equatorias da ke kudancin kasar, wadanda suka gaji da salon mulkin Silva Kiir.

Mr Biong ya ce: "Kamata ya yi a rusa gwamnati a kafa gwamnatin hadaka a Juba karkashin jagorancin SPLM wacce za ta gudanar da zaben 2015, ta saki dukkan tsararru ta kuma yi kokarin sasanta rikicin SPLM."

Sai dai hakan da kamar wuya.

Mataki na gaba na iya zama na soji, inda bangarorin biyu za su gwada karfinsu.

Duk wannan dai na faruwa ne sakamakon yakin da aka yi shekaru ana yi a Sudan ta Kudu, da kuma kwadayin mulki tsakanin 'yan siyasar kasar, tare da tsananin kabilanci da yawan 'yan bindiga a cikin al'umma.

Shekaru biyu da samun 'yancin kai, Sudan ta Kudu na fuskantar mafi munin halin da ake guje mata.