Uganda ta haramta luwadi da madigo

Image caption 'Yan luwadi da madigo na fuskantar daurin rai-da-rai.

Majalisar dokokin Uganda ta zartar da dokar haramta luwadi wacce ta jawo cece-kuce.

Dama dai luwadi da madigo haramun ne a Uganda amma sabuwar dokar ta tanadi hukuncin daurin rai da rai ga masu wannan dabi'a.

Haka kuma dokar, wacce masu gwagwarmaya ke cewa ta yi tsauri da yawa, ta haramta abinda ta kira yada luwadi da madigo.

Mutanen ma da suka shaida ana wannan dabi'a ba su sanar da 'yan sanda ba za su fuskanci hukunci dauri.

Daftarin dokar na farko ya tanadi hukuncin kisa ga 'yan luwadi da madigon amma daga baya aka sauya.