Obama zai canza aikin hukumar leƙen asiri

Image caption Shugaba Obama na Amurka

Shugaba Barak Obama ya ce zai shafe makwanni na gaba yana duba yadda za a iya yi wa Hukumar Tsaron Kasar garambawul.

Obama yace, za a yi gyaran da zai bai wa Amurkawa karin kwarin gwiwa kan ayyukan hukumar leken asirin.

Shugaban Amurkan ya yi wadannan kalaman ne a dai dai lokacin da tsohon ma'aikacin leken asirin Amurkan Edward Snowden ya sake fitar da wasu takardun bayanan sirri.

Wani kwamiti da shugaba Obaman ya kafa ya ba da shawarwari da suka hada da cewa hukumar tsaron kasar ta dena tara dimbin bayanan wayoyin jama'a.