Ana ci gaba da gumurzu a garin Bor na Sudan ta Kudu

'Yan gudun hijira a Sudan ta Kudu
Image caption 'yan gudun hijira a Sudan ta Kudu

Dakarun Sudan ta Kudu na kokarin sake kwace iko da muhimmin garin nan na Bor, kwanaki uku bayan sojojin dake biyayya ga tsohon mataimakin shugaban kasar sun kwace iko da shi.

Garin na Bor shi ne hedkwatar jihar Jonglei, daya daga cikin yankunan da aka fi samun barkewar rikici a kasar.

Mutane sama da dari biyar ne aka kashe a rikicin kabilancin, tun daga ranar Lahadi, lokacin da shugaba Salva Kiir ya zargi tsohon mataimakinsa Riek Machar da kulla makarkashiyar juyin mulki.

Akwai rahotannin dake cewa an harbi wasu jiragen saman Amurka a kusa da garin na Bor, yayinda suke kokarin kwashe 'yan kasar Amurka.