Sojoji na hangen barkewar yakin basasa a Thailand

Image caption Jam'iyyar da ke mulkin kasar dai ta nace kan cewa zabe ne kawai zai iya raba gardama kan wanda ya dace ya mulki kasar.

Kwamandan rundunar Sojan kasar Thailand ya yi gargadin cewar yakin basasa zai iya barkewa a kasar idan aka gudanar babban zabe kamar yadda aka tsara a watan Febrairu saboda halin zaman tankiya da fagen siyasar kasar ke ciki.

Janar Prayuth Chan-Ocha ya ba da shawarar a jinkirta gudanar da zaben domin a ba gwamnati da abokan hamayyarta damar zaunawa su tattauna kan bambamce-bambancensu.

Tun ba yau ba ne dai rundunar sojan ke sa bakinta a cikin sha'anin siyasar kasar, sai dai ya zuwa yanzu ba ta dauki bangare ba a takaddamar da ake yi tsakanin gwamnati da masu zanga-zanga da ke kokarin kifar da ita.

Yanzu da kusan wata daya ke nan da dandazon jama'a masu adawa da gwamnati suke ta yin gangami a Bangkok babban Birnin Kasar; a wani yunkuri na kifar da gwamnatin ta Farayin Minista YingLuck Shinawatra.

Karin bayani