'Yan adawa sun ce ba zasu shiga zaben Thailand ba

Masu zanga zanga a Thailand
Image caption Masu zanga zanga a Thailand

Babbar jam'iyyar adawa a Thailand ta Democrats ta ce ba zasu su shiga zaben da za a gudanar ba a watan Fabrairu mai zuwa ba, a wani mataki da ake ganin zai kara dagula al'amurra a rikicin siyasar da kasar ke ciki.

Praminista Yingluck Shinawatra ta bada sanarwar za a yi zaben kasa ne, bayan jerin zanga zanga a Bangkok, babban birnin kasar, inda masu zanga zangar ke kiran da ta sauka.

Jam'iyyar Ms Yinluck ce ta samu gagarumar nasara a zaben na baya, kuma ana hasashen cewa ita ce zata sake yin galaba, idan aka yi sabon zabe.