Masar: An yanke wa masu fafutuka hukunci

Image caption Masu fafitikar uku a gaban kuliya

Wata kotu a Alkahira, babban birnin kasar Masar, ta yanke hukuncin daurin shekaru uku, da aiki a mai tsanani, a kan wasu fitattun masu rajin kafa dimokradiyya su uku.

An dai yanke musu wannan hukunci ne saboda rawar da suka taka a jerin zanga zangar da aka yi a baya bayan nan.

Ɗaya daga cikin lauyoyin wanɗanda aka ɗaure Waleed AbduRauf, ya ce, an mayar da wannan hukunci na siyasa, kuma manufar ita ce a aike da sako ga daukacin matasan kasar Masar.

Mutanen uku sun kasance a kan gaba cikin kungiyar da ta iza wutar tarzomar da aka yi a 2011, da yayi sanadiyar kifar da gwamnatin Shugaba Hosni Mubarak.