Kenya: Jirgin ƙasa ya yi haɗari

Ma'aikatan agaji na fargabar cewa mai yuwuwa akwai wasu mutane da aka rutsa da su a baraguzan jirgin kasan da ya kauce daga layin dogo.

Lamarin ya auku ne a wata anguwa ta masu ƙaramin ƙarfi, dake Nairobi, babban birnin kasar.

Wani jami'in 'yan sanda ya ce, ya zuwa yanzu mun zakulo mutane kimanin shidda, kuma dukkansu suna numfashi, a halin da ake ciki.

Mutane a ƙalla bakwai ne aka tabbatar da sun jikkata lokacin da taragwai hudu na daukar kaya suka afka kan wasu gidaje dake kusa da layin dogon.

Ma'aikatan ceto na ta kokarin samun hanya ne a wannan anguwa dake cike da jama'a domin shigar da na'urorin da za a daga taragwan, domin kaiwa ga wadanda aka danne.