Wasu 'yan Nijeriya a Saudiyya sun yi ƙorafi

Image caption 'Yan kasashe da dama ne suka fice daga Saudiyya

Wasu 'yan Najeriya a Saudiyya sun koka akan halin da suke ciki a inda ake tsare da su tun bayan sun mika kansu domin a maida su gida, sun kuma zargi gwamnatin Najeriya da yin watsi da su.

Gwamnatin Saudiyyar ce dai ta bukaci duk baki da basu da takardu su fice daga cikin kasar.

'Yan Najeriyar sun ce, suna cikin wani hali, kuma har yanzu ba su ga alamun gwamnatin Najeriya zata maida su gida ba.

Sai dai kuma jakadan Nijeriya a Jeddah ya ce, suna daukar matakan tabbatar da an kwashe 'yan Nijeriyar zuwa gida.

Ya kuma ce, suna kula da 'yan Nijeriyar a inda suke tsare.