Apple ya hada kai da China Mobile

Apple a China
Image caption Apple na neman karbuwa a China.

Kamfanin Apple na Amurka ya kulla yarjejeniyar sayar da wayar iPhone ta hannun kamfanin wayar salula na China Mobile, wanda shi ne yafi kowanne girma a duniya.

Kamfanin China Mobile na da abokan hulda fiye da miliyan 760 kuma ya na cikin kamfanonin China uku da aka bai wa lasisin samar da intanet samfurin 4G.

Apple na kokarin habaka cinikinsa a China, wacce ta zarta kasashen duniya wurin amfani da wayoyin komai-da-ruwanka, amma ya na gwagwagwa da sauran kamfanonin kera wayoyin.

Babu arha

Fiye da mutane biliyan 1.2 ne ke amfani da wayoyin komai-da-ruwanka a China amma cinikin iPhone ya ja baya sanadiyyar karbuwar wayoyi masu arha irinsu Samsung, Lenovo da Coolpad.

Kasuwar Apple ta yi kasa ne saboda sabanin kasashen da suka ci gaba, a kasashe masu tasowa kamfanin wayar salula ba sa rage kudin wayoyin koma-da-ruwanka.

Hakan na nufin wajibi ne masu saye su biya kudin wayar nan take, abinda ke sa kayan Apple ke yi wa mutane tsada.

Domin shawo kan matsalar ne Apple ya fitar da samfurin iPhone 5c mai arha a farkon shekarar nan.

Babbar dama

Image caption China ce babbar kasuwar wayar salula a duniya.

Manazarta sun ce saukaka farashin wayar tare da hada kai da kamfanin wayar salula mafi girma a duniya babbar dama ce ta bunkasa cinikin Apple.

Kamfanin Cantor Fitzgerald ya kiyasta Apple na iya sayar da wayoyin iPhone miliyan 24 ga abokan huldar China Mobile kadai a badi.

A watanni taran farkon shekarar nan dai Apple ya sayar da wayoyin iPhone miliyan 102.4 ne.

Daga 17 ga Janairu ne masu layin China Mobile za su fara amfani da wayoyin iPhone 5s da 5c.