Shekara guda da shigar Afrika ta Tsakiya rudani

Image caption Afrika ta TSakiya ta cika shekara da shiga rudani

Kusan shekara guda ke nan da Jamhuriyyar Afrika ta Tsakiya ta fara shiga rudani.

Shekara ta 2013 ta kasance shekarar da Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya ta rika fuskantar tashe-tashen hankula da aka soma da boren gungun kungiyoyi da suka hade da ake kira SELEKA wanda suka yi a watan disambar bara.

Duk da cewa an yi ta tattaunawar neman sulhu da kuma yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma a Libraville, 'yan tawayen sun hambarar da gwamnatin shugaba Francois Bozize lokacin da suka far wa Bangui babban birnin kasar a ranar 24 ga watan Maris, lamarin da ya tilasta masa samun mafaka a makwabciyar kasar wato Kamaru.

Kungiyar ta Seleka dai na ikirarin cewa ta na wakiltar kungiyoyin 'yan bindiga biyar da ke zargin shugaba Bozize da karya yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a Libraville a shekarar 2008.

Karin bayani