Bam ya kashe mutane fiye da 14 a Masar

Image caption Ana samun karuwar harin bam a Masar

Wani harin bam din mota da aka kai a shalkwatar 'yan sanda da ke arewacin Masar ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla goma sha hudu tare da raunata wasu fiye da dari.

Harin wanda aka kai a garin Mansoura ya haddasa rushewar wani bangare na wani gini mai hawa biyar.

Wasu rahotanni sun ce akwai fashewar abubuwa da dama.

Yawan kai hare-hare kan jami'an tsaro a Masar na kara yawaita tun bayan da aka hambare gwamnatin shugaba Morsi a watan Yulin da ya gabata.

Karin bayani