Jirgin sama ya zunguri gini a Afrika ta Kudu

Image caption Duk fasinja sun tsira amma mutane hudu a kasa sun ji rauni.

Wani jirgin sama dauke da fasinjoji fiye da 200 ya dunguri gini yayin da ya ke kokarin tashi daga birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu.

Jirgin na British Airways mai zuwa London na shirin tashi ne daga filin jiragen sama na OR Tambo, lokacin da fiffikensa na dama ya zunguri ginin, tare da raunata mutane hudu da ke cikin ginin.

Hukumar sufurin sama ta Afrika ta Kudu ta ce titin ne ya yi jirgin siranta.

A cewar hukumar tuni aka janye jirgin kuma an ci gaba da zirga-zirga a filin.

Shi kuma kamfanin British Airways ya ce ya tsugunar da fasinjojin 182 a otal kuma ana kokarin samar da wani jirgin da zai yi jigilarsu.