Obasanjo ne ya wargaza PDP - Jonathan

Image caption Wannan wasikar dai martani ne da 'yan Najeriya da dama ke dako daga Shugaba Jonathan.

Shugaban Najeriya Dr. Goodluck Jonathan ya ce tsohon shugaban kasar Cif Olusegun Obasanjo ne ya rusa jam'iyyar PDP ba shi ba.

Shugaba Jonathan ya ce cif Obasanjo bai yi ma sa adalci ba a zarge-zargen da suka shafi rashin cika alkawari da rashin iya jagoranci da wasu matsaloli da ka iya wargaza kasar, a cikin budaddiyar wasikar da ya aike masa.

A cikin wata wasika mai shafi 14, Mr. Jonathan ya ce tsohon shugaban bai kyauta masa ba ko kadan sakamakon zarge-zargen da ya jera masa wadanda ya ce ba su da tushe ba; kuma a cewarsa, mafi yawan matsalolin da Cif Obasanjo ya lissafa sun samo asali ne daga gwamnatocin da suka gabaci tasa cikin har ta- shi Obasanjon.

''Wani batu da shugaban jonathan ya dauki lokaci mai tsawo yana mai da martani kansa shi ne zargin cewar yana horar da wasu 'yan daba yadda ake sarrafa bindiga domin yakar masu adawa da shi; inda ya kalubalanci Cif Obasanjon da ya rantse da littafin Bible idan ya yarda wannan zargin gaskiya ne'' inji wani wakilin BBC da ya ga wasikar.

Karin bayani