Mutumin da ya kirkiro bindigar AK 47 ya mutu

Image caption Mikhail Kalashnikov ya kera bindigogin da Rasha ta yi amfani da su.

Mutumin da ya kirkiro da bindiga AK 47, Mikhail Kalashnikov ya rasu yana da shekaru 94, kamar yadda kafafen yada labarai na Rasha su ka bayyana.

Bindigar da ya kirkiro ta kasance makamakin da aka fi amfani da shi a duniya.

Saboda saukin sarrafawa da kuma saukin farashi, ya sa duniya ta raja'a a kanta.

Duk da cewar an martabashi a kasar sa, Kalashnikov ya bayyana cewar bai samu wani kudin kirki ba daga kirkiro bindigar.

An kwantar da Mikhail Kalashnikov a asibiti ne a watan Nuwamba sakamakon jinin dake zuba masa a cikin jikinsa.

An haifeshi a ranar 10 ga watan Nuwambar shekarar 1919 a gabashin Siberia, kuma daya ne daga cikin 'ya'ya 18 da iyayensu su ka haifa a kauyen Altai mai cike da tsaunuka.

Karin bayani