Likitoci sun koma aiki a Nigeria

Image caption Rashin kayan aiki na damun likitoci a Nigeria.

Da safiyar Litinin din nan ne likitoci a Nigeria su ka koma bakin aiki bayan gudanar da yajin aikin gargadi.

Shugaban kungiyar likitocin Dr Osahon Enabulele ya ce kungiyar ta dakatar da yajin aikin ne saboda shagulgulan kirismeti.

Dr Enabulele ya ce kungiyar za ta shiga yajin aikin sai-baba-ta-gani ranar Litinin 6 ga Janairun badi idan gwamnatin kasar ba ta biya mata bukatunta ba.

Bukatun kungiyar dai sun hada da biyan alawus ga likitoci, ba su ingantaccen horo, samar da kayan aiki ga asibitoci da kuma samar da inshorar kiwon lafiya ga daukacin 'yan kasar.

Gwamnatin Nigeria ta ce ta na daukar matakan biyan bukatun likitocin.

Karin bayani