An daure tsohon minista a Britaniya

Image caption Denis MacShane ya yi aringizon kashe kudaden gwamnati.

An yanke wa wani tsohon ministan Britaniya Denis MacShane hukuncin daurin watanni shida saboda cuwa-cuwar $21,000 kusan Naira miliyan hudu.

Tsohon ministan ya amsa laifin cewa ya mika wa gwamnatin rasitan bogi 19 na biyan ayyukan bincike da fassara.

Mutumin mai shekaru 65 shi ne dan majalisar dokokin Britaniya na biyar da aka yankewa hukuncin dauri tun bayan fallasa badakalar zulaken kudaden batarwa a shekarar 2009.

MacShane ya yi dan majalisa ne a jam'iyyar Labour tsawon shekaru 18 kuma shi ne ministan harkokin nahiyar Turai zamanin mulkin Tony Blair.