Sojoji sun kashe 'yan Boko Haram 50

Image caption Sojojin Nigeria

Rundunar Sojin Nigeria ta ce ta kashe 'yan Boko Haram 50 lokacin suna kokarin tsallakawa daga kan iyakar kasar zuwa Kamaru a wani gumurzu da su ka yi a ranar Litinin.

A cewar kakakin rundunar tsaron, Birgadiya Janar Chris Olukolade, sojoji 15 da fararen hula biyar suma sun rasu sakamakon musayar wuta tsakaninsu da 'yan kungiyar.

Dakarun Nigeria sun kara azama wajen farautar 'yan Boko Haram cikin 'yan kwanakinnan tun bayan da 'yan kungiyar suka kai hari a barikin sojoji dake garin Bama a ranar Juma'ar da ta gabata.

Janar Olukolade ya kara da cewar sun lalata motocin 'yan Boko Haram 20 wadanda aka yi amfani dasu wajen kaddamar da hari a barikin sojojin na Bama.

Mazauna Bama sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewar 'yan kungiyar sun yi awon gaba da matan sojoji da 'ya'yansu da dama lokacin harin na ranar Juma'a.

Karin bayani