'Yan bindiga sun kashe mutane 6 a Filato

Image caption Taswirar Nigeria

Rahotanni daga jihar Filato a arewa ta tsakiyar Nijeriya na cewa an kashe akalla mutane shida tare da jikkata wasu karin biyar a wani hari da wasu 'yan bindiga su ka kai a karamar hukumar Barkin Ladi.

A baya-bayan nan dai koda yake an samu kwarkwaryar zaman lafiya a Jos babban binrin jihar, amma ana samun kashe-kashe jefi-jefi a wasu kauyuka dake kewayen birnin, kuma lamuran na zuwa ne yayin da ake ci gaba da kokarin sasanta al'umomin na jihar ta Filato da suka dade suna samun rashin jituwa a tsakaninsu.

Kawo yanzu dai ba a tantance ko su wane ne maharan da suka kashe mutanen yankin Foron kuma rahotanni na cewa yan bindigar sun sulale ne bayan da suka kaddamar da harin a daren Litinin.

Mista Rwang Dantong, shugaban matasan kabilar Berom ta kasa, ya shaidawa BBC cewa lamarin ya rutsa da mutanen ne a gidajnesu.

Jami'an tsaro a Filato basu fidda sanarwa kan lamarin ba.

Karin bayani