'Sojojinmu sun kwace iko da Bor'- Kiir

Salva Kiir
Image caption Salva Kiir ya ce yanzu sojojinsa na iko da Bor

Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir, ya ce dakarun gwamnatinsa sun sake kwace iko da muhimmin garin Bor dake Arewacin Juba babban birnin kasar.

Mr Kiir ya ce a yanzu haka dakarun gwamnati ne ke tafiyar da garin, wanda sojoji masu goyon bayan tsohon mataimakin kasar, Riek Machar suka kwace a kwanakin baya.

Hakan dai ya biyo bayan bayanin da Ofishin kwamishinan Majalisar Dinkin Duniya mai kula da kare hakkin bil'adama ya yi ne na cewa wata tawagar masu bincike sun gano wani babban kabari a Sudan ta Kudun.

Wata mai magana da yawun majalisar dinkin duniyar ta ce kabari daya ya kunshi gawawwaki goma sha hudu a garin Bentiu da ke jahar Unity, kuma an kuma gano wasu gawawwakin a bakin kogi, amma da fari ta ce gawawwakin sun kai saba'in da da biyar.

Karin bayani