West Ham na zawarcin Asamoah Gyan

Image caption Asamoah Gyan

Sam Allardyce ya ce West Ham na duba yiwuwar sayen dan kwallon Ghana Asamoah Gyan a watan Junairu mai zuwa.

Allardyce na bukatar dan kwallon gaba saboda raunin Andy Caroll.

Wakilin Gyan ya ce West Ham na shirin siyo dan kwallon a matsayin aro.

Gyan mai shekaru 28, ya koma Sunderland a shekara ta 2010 a kan fan miliyan 13 kafin ya hade da kungiyar Al_Ain ta Dubai a shekara ta 2012.

Karin bayani