Bom ya kashe mutane 34 a Iraq

Ana yawan kai wa Kiristoci hari a Iraq
Image caption Ana yawan kai wa Kiristoci hari a Iraq

Akalla mutane 34 ne suka mutu a hare-haren bom guda biyu da aka kai wa Kiristcoci a Bagadaza, babban birnin Iraq.

A harin farko, wani bom da aka dasa cikin mota ya tashi lokacin da masu bauta ke fitowa daga coci, inda ya hallaka akalla mutane 24.

Wani bom din kuma ya fashe a kasuwar wata unguwar Kirista da ke kusa da cocin, inda ya hallaka mutane 10.

Ana fargabar adadin wadanda suka rasu zai iya karuwa saboda akwai wadanda su ke cikin halin mutu-kwakwai-rai-kwakwai.

Kawo yanzu babu wanda ya dau alhakin kai hare-haren.