Jihar Kano ta mai da ilimi kyauta

Rabiu Musa Kwankwaso
Image caption Rabiu Musa Kwankwaso

Gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Nigeria ta kaddamar da tsarin ba da ilimi kyauta ga daliban jihar daga matakin piramare har zuwa jami'a.

Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso ne ya bayyana haka a jawabin da ya gabatar ranar Talata na kasafin kudin badi ga majalisar dokokin jihar.

Ya ce hakan ya biyo bayan kudirin gwamnatinsa na bunkasa ilimi a fadin jihar.

Kasafin kudin na Naira biliyan 219 ya kunshi sababbin ayyuka na kaso 68% ne yayin da ayyukan yau da kullum za su kwashe kaso 32%.