Kotu ta ki dakatar da auren jinsi a Utah

Image caption An daure aure 700 tsakanin 'yan luwadi da madigo a Utah daga Juma'a zuwa Laraba.

Wata kotun tarayya a Amurka ta yi watsi da bukatar gwamnatin jihar Utah ta neman tsayar da aure tsakanin jinsi guda a jihar.

Gwamnatin ta bukaci a dakatar da aure tsakanin jinsi guda a jihar har sai an kammala sauraron karar da ta daukaka bayan da wani alkali ya soke dokar da ta haramta auren jinsi guda a jihar.

Kimanin 'yan luwadi da madigo 1,400 ne suka daure aure a jihar bayan watsi da bukatar gwamnatin ranar Juma'a.

Masu aiko da rahotanni sun ce hukuncin kotun na da muhimmanci, domin zai jawo kotun kolin Amurka ta dauki matakin da zai yi aiki a fadin kasar.