Ministoci uku sun ajiye aiki a Turkey

 Erdogan Bayraktar
Image caption Ministan muhalli mai murabus Erdogan Bayraktar

Ministocin Turkey guda uku sun yi murabus kwanaki kadan bayan da aka kama ya'yansu a wani babban binciken cin hanci a wani bankin gwamnati.

Na baya bayan nan da yayi murabus shi ne ministan muhalli da raya birane, Erdogan Bayraktar, wanda aka tsare dansa na wani dan gajeren lokaci a binciken cin hancin cikin makon da ya wuce.

Da safiyar Laraba ne ministan raya tattalin arziki, Zafer Caglayan da kuma ministan cikin gida, Muammer Guler su ka yi murabus.

Ya'yan ministocin na daga cikin mutane 24 da aka bincika a makon da ya gabata saboda zargin karba ko kuma bayar da cin hanci.

Ministocin wadanda su ba a zarge su ba, sunce ya'yan nasu ba su da laifi.