Papa Roma ya koka da rikici a sakon Xmas

Image caption Papa Roma Francis tare da mutum-mutumin jinjirin Yesu.

Papa Roma Francis ya yi magana game da yankunan da ke fama da rikici a fadin duniya, a jawabinsa na Kirismeti na farko daga birnin Rum.

Ya bukaci bangarorin da ke yaki a Syria su bada damar kai agaji baki daya sassan kasar.

Ya kuma yi kira da a tsagaita wuta a Sudan ta Kudu, tare da neman shugabannin duniya da su kare mai da hankali kan rikicin jamhuriyar Afrika ta tsakiya, wanda ya ce ba'a cika kula da shi ba.

Da ya juya kan batun daruruwan masu kaura daga Eritrea da suka nutse kusa da tsibirin Lampedusa a Oktoba, Papa Roman ya bayyana damuwarsa kan kuncin da kan jefa mutane cikin halin da za su iya kantafi da rayukansu.