Bom ya tashi a Masar

Image caption 'Yan sanda kusa da wurin da bom ya tashi a Masar.

Mutane biyar sun samu rauni bayan da bom ya fashe kusa da wata motar haya a Cairo, babban birnin Masar.

Ma'aikatar lafiya ta Masar ta ce babu wanda ya rasu.

Jami'an tsaro sun ce an dasa bom din ne a gefen hanya kuma ya fashe lokacin da motar hayar ta wuce a gundumar Nasr City da ke arewacin birnin.

Bom din ya fashe ne kwana guda bayan da gwamnatin kasar ta bayyana kungiyar 'Yan Uwa Musulmi a matsayin 'yan ta'adda.

Jami'an tsaro sun kuma kwance wani bom din kafin ya tashi bayan da aka dasa shi cikin wani allon talla da ke kusa da inda bom din farko ya tashi.