An kwace ikon garin Kamango a Congo

Image caption Ikon Kamango ya dawo hannun Congo

Sojojin Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo tare da taimakon dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya sun kwace ikon garin Kamango da ke kasar.

Garin wanda ke kusa da Uganda, na karkashin ikon masu kaifin kishin islama na kasar, inda a harin da sojojin suka kai a safiyar Laraba suka kwace ikon daga hannunsu.

Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya sun yi amfani da jirgi mai saukar ungulu wajen kai wa 'yan tawayen hari bayan da sojojin Congon suka bukaci daukinsu.

Yanzu haka dai 'yan tawayen sun nufi garin Nobili wanda ke kan iyaka da Uganda wajen kuma da dubban al'ummar kasar suka mai da shi sansanin 'yan gudun hijra sakamakon rikicin da ake yi a kasar.

Karin bayani