Fulani sun ja kunnen gwamnatin Nigeria

Image caption Ana korar Fulani daga wasu jihohi na Nigeria.

Kungiyar Fulani makiyaya ta Nigeria, Miyetti Allah ta baiwa gwamnatocin kasar wa'adin makonni biyu da su gaggauta kawo karshen abin da suka kira cin mutunci da suke zargin ana yi musu a wasu jihohin kasar.

A wani babban taro da tayi da manema labarai a birnin Lagos, kungiyar tace korar Fulani da ake yi daga matsugunnin da suke a jihar Kogi da wasu jihohi ba karamin tauye hakkinsu ba ne.

Shugaban kungiyar na kasa Alhaji Bello Bodejo ya ce idan jihohin kudancin kasar ba su daina korar Fulani kafin cikar wa'adin ba, za su sake zame domin tsayar da matakin da za su dauka na magance matsalar.

Ana yawan samun hatsaniya tsakanin Fulani makiyaya da manoma a sassan Nigeria da dama.