Masar ta kama 'yan uwa Musulmi 16

Image caption Kungiyar 'yan uwa Musulmi na da dimbin magoya baya.

Mahukuntan Masar sun kama magoya bayan haramtacciyar kungiyar 'yan uwa Musulmi akalla 16, kwana guda bayan da suka bayyana ta a matsayin kungiyar 'yan tawaye.

Wandanda aka kama sun hada da dan mataimakin shugaban kungiyar, wacce aka kifar da ita daga mulki lokacin da sojoji suka hambarar da shugaba Muhammad Morsi a watan Yuli.

Kamfanin dillancin labaran Masar ya ce an kama su ne bisa zargin yada akidar kungiyar tare da zugar kai hare-hare kan sojoji da 'yan sanda.

Da safiyar Alhamis ne dai wani bom da aka dana wa motar haya a birnin Cairo ya raunana mutane biyar.