2013: Shekarar tafi-da-gidanka

Image caption Rayuwar tafi-da-gidanka

Wannan ce shekarar da duniya ta koma tafi-da-gidanka. Ba kuma wai kawai maganar wayoyin komai da ruwanka da kwamfutocin hannu ba.

Magana ce ta aikin tafi-da-gidanka in da ma'aikata ke amfani da wayoyinsu wurin ci gaba da ayyukansu a ciki da wajen ofisoshinsu.

Magana ce ta adana bayanai da kuma yada su ta hanyar tafi-da-gidanka; tsarin tafiyar da kamfanoni bisa tafarkin hadaka.

A takaice dai, a bana tafi-da-gidanka ya zarta na'ura ya zama tsarin rayuwa.

Sabon tsari

Wanann sabon tsarin, wanda ya biyo bayan samuwar fasahar intanet mai sauri ta 4G, ya kawo kalubale da damarmaki ga harkokin kasuwanci.

David Chan na jami'ar kasuwanci ta Cass dake London na ganin na'urorin tafi-da-gidanka sun kawo kwakkwaran sauyi kan yadda mu ke tafiyar da rayuwarmu - yadda mu ke aiki, ciniki, kirkira da sadarwa - sai dai kamfanoni da yawa an bar su a baya wurin wannan sauyin.

Rushewar manyan kantuna a kasashen da suka cigaba ya isa misali kan yadda mutane suka koma sayen kayayyaki ta hanyar wayoyinsu.

Zamanin hadaka

A 2013, an yi amfani da wayoyin komai da ruwanka masu dauke da fasahar GPS, kyamara, agogo, da kuma intanet ta sababbin hanyoyi da dama.

Image caption An yi amfani da na'urorin tafi-da-gidanka a kiwon lafiya.

A shekarar ne aka koma amfani da wayoyin salula wurin gwada bugun zuciya da hawan jini, tare da tattara bayanan, dora su a intanet, da kuma yada wa ga abokan hulda.

Ta wannan tsarin na hadaka, an samu nasarori a fannin aikin injiniya da binciken kimiyya tsakanin mutanen da ke zaune a kasashe mabambanta.

Ambaliyar bayanai

Image caption Ana iya sarrafa na'urorin gida da tafi-da-gidanka

Daga kan kwayoyin da za su aika maka sakon waya idan lokacin sha ya yi, zuwa ga na'urorin sanyaya daki da za'a iya sarrafa wa daga nesa ta hanyar wayar salula, na'urorin tafi-da-gidanka sun kawo sauye-sauye a bana.

Sai dai duk wadannan na'urorin na tara dimbin bayanan da ake bukatar adana su da kuma boye su daga 'yan sa ido.

An samar da manahajar kwamfuta da ke iya nazarin wadannan bayanai domin 'yan kwana-kwana su gano wuraren da suka fi shiga hatsarin gobara; 'yan sanda su gano irin dabi'un da za su ba da damar kama ma su laifi; sannan cibiyoyin hada-hadar kudi su yi nazarin hirarrakin waya domin gano 'yan cuwa-cuwa.

Barazanar tsaro

Sai dai kuma hakan ya ba wadanda suka mallaki fasahar damar leka asirin hukumomi, kamfanoni da mutane kamar dai yadda fallasar da Edward Snowden ya yi wa hukumar leken asiri ta Amurka, ta tabbatar.

Barazana daga masu satar bayanai da hakkin mallaka, 'yan cuwa-cuwa da 'yan leken asiri ta karu a cikin 2013.

Image caption An yi yamadidi da barazanar tsaro a 2013

Kuma yaduwar tsarin tafi-da-gidanka ya kara ta'azzara lamarin.

Kamar dai yadda Steve Prentice na kamfanin bincike na Gartner ya fada tun watan Janairu; "za'a samu karuwar na'urorin tafi-da-gidanka masu dauke da manhajoji iri-iri, da za su ba da damar karin shiga intanet, cefane ta waya, da kuma yada bayanai ga abokananmu na shafukan sada zumunta. Wadannan duk su na iza bukatar karin saurin intaent da kuma yada ta zuwa kowanne lungu da sako na duniya."

Wannan ita ce 2013: shekarar da duk muka zama tafi-da-gidanka.