Sudan ta Kudu: Faɗa ya ƙara ƙazancewa

Image caption Shugabannin Kenya da Habasha tare da shugaba Kiir

Ƙazamin faɗa ya ci gaba tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan tawaye a Sudan ta Kudu.

Wakiliyar majalisar dinkin duniya ta musamman a can, Hilde Johnson ta ce, mutane fiye da dubu daya ne aka kashe.

Koda yake har yanzu babu hakikanin adadin mutanen da aka kashe.

Shugabannin Afrika sun sake sabunta kokarinsu na shiga tsakanin Shugaba Salva Kiir da abokan hamayyarsa.

Shugaba Kiir ya gana da Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta, da kuma Pirayim Ministan Ethiopia Hailemariam Desalegn.

Rahotanni sun ce sun tattauna a kan matsalar da jama'a ke ciki da kuma yiwuwar tsagaita wuta.

Ba a sani ba dai ko za su gana da abokin adawar Shugaba Kiir, wato Riek Machar.