Ana ci gaba da yaki a Sudan ta Kudu

Image caption Rikicin Sudan ta Kudu ya rutsa da mutane da dama.

Ana ci gaba da kazamin fada tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawaye a Sudan ta Kudu yayin da shugabannin kasashen Afrika ke kokarin sasantawa tsakanin shugaba Salva Kiir da abokan hamayyarsa.

Wani kakakin soja ya ce su na shirin kai hari domin kwato Bentiu, babban birnin jihar Unity, mai arzikin man fetur, wacce ke hannun 'yan tawaye.

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta da Pirai ministan Ethiopia Hailemariam Desalegn ne ke jagorantar yunkurin sasantawar.

Sai dai tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar ya ce ya na bukatar a saki manyan magoya bayansa kafin ya shiga tattaunawar.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce dubunnan mutane sun bar gidajensu sakamakon rikicin.