"Taliban na iya kwatar garuruwan Afghanistan"

Image caption Mayakan Taliban a Afghanistan

Shugaban sojin Britaniya ya yi gargadin cewa 'yan Taliban za su iya kwace muhimman yankunan Afghanistan bayan janyewar sojojin kasashen waje a badi.

Sir Peter Wall ya shaida wa jaridar the Telegraph ta Britaniya cewa 'yan bindiga na iya yunkurin kwace garuruwan da suka mallaka a baya irin su Musa Qala dake kudancin kasar.

Bayanin nasa ya biyo bayan makamantansa daga wasu kwamandojin na rundunar NATO.

Sai dai Sir Peter Wall ya ce Britaniya ta cika aniyarta ta tarwatsa Al Qaeda a Afghanistan.

Karin bayani