"A hukunta wadanda suka yi kisan Apo"

Image caption Kisan Apo a Abuja na damun matasa

Wata kungiyar tabbatar da hakkokin matasa da ake kira CHYDAN ta nemi gwamnatin Najeriya da ta hukunta jami'an tsaron da suka kashe matasan nan takwas a unguwar Apo a Abuja a watannin baya.

Kungiyar ta ce dole ne a hukunta wadanda suka yi kisan dan ya zama darasi ga sauran jami'an tsaro.

Jami'an tsaron Najeriya dai sun bude wa matasan wuta ne da daddare bisa zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne.

Kungiyar ta ce barzanar da ja'mian tsaro ke yi wa matasa na jefa shakku kan yadda kasar ke gudanar da dimokradiyya.

Karin bayani