Mu muka kai harin Bama - Shekau

Image caption Imam Abubakar Shekau ya ce sun kashe mutane da yawa a harin barikin Bama a arewa maso gabashin Nigeria.

Shugaban kungiyar Jama'atu Ahlul Sunna Lid-Da'awati wal Jihad, wadda ake kira Boko Haram, Abubakar Shekau ya ce kungiyar ce ta kai harin nan na ranar 20 ga Disamba a barikin sojojin da ke Bama a yankin arewa maso gabashin Nigeria.

Shugaban kungiyar ya bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo da ya fitar wanda kuma kamfanin dillacin labarai na AFP ya samu.

A yayin da yake zaune a kan wata tabarma, zagaye da wasu mambobin kungiyar dauke da makamai, Imam Abubakar Shekau, ya ce mayakansa ne suka afkawa barikin sojojin na Bama, yana mai cewar sun lalata tankokin sulke 21 sannan kuma sun hallaka mutane masu yawa.

Gabanin asubahi ne dai wasu 'yan bindiga, cikin jerin gwanon motoci suka afkawa barikin sojojin na Bama, inda suka budewa sojoji wuta sannan suka bankawa barikin wuta bayan harin.

Wata sanarwa da ma'aikatar tsaron Nigeria ta fitar, ta ce sojoji sun kashe wadanda ta kira 'yan ta'adda 50 a yayin da su ke bin sahun wadanda suka kai hari zuwa barikin na Bama, inda kuma ta ce sojoji 15 ne suka rasa rayukansu a harin tare da farar hula biyar.

Karin bayani