China ta amince da haihuwar da fiye da daya

China
Image caption A baya dokar takaita haihuwa na aiki ka'in da na'in a China

Kasar China ta amince da dokar da za ta bawa ma'aurata damar haifar da fiye da daya.

Dokar ta bada damar haifar da fiye da daya matukar daya daga cikin ma'auratan shi kadai iyayyensa suka haifa.

An dai sanar da sauya tsarin karin haihuwar ne bayan tattaunawar da jami'an Jam'iyyar Kwamunis suka yi a watan Nuwambar da ta gabata.

Haka kuma an amince da soke tsarin nan na horar da mutane, ta hanyar aikin tilas.

A baya dai dokar takaita haihuwa na aiki ka'in da na'in a kasar ta China.

Karin bayani