Bom ya jikkata mutane shida a Kabul

Image caption Harin kunar bakin wake kan dakarun NATO a Kabul.

'Yan sanda a Kabul babban birnin Afghanistan sun ce fararen hula shida sun samu raunuka sanadiyyar harin kunar bakin wake kan wani jerin gwanon motocin dakarun NATO.

Maharin ya dasa bom din ne cikin motarsa a kan wata babbar hanya da ke kusa da sansanin sojojin NATO a gabashin Kabul.

'Yan Taliban sun ce su suka kai harin.

Kakakin rundunar ta NATO ya ce su na gudanar da bincike game da harin.