An sako dan Lebanon da aka sace a Kano

Image caption Jihar Kano ce tafi kowacce yawan al'umma a Nigeria.

Rahotanni daga jihar Kano a arewacin Nigeria na cewa an sako dan kasuwar nan dan kasar Lebanon da aka sace ranar Litinin.

An dai sako Hasan Zain da safiyar Juma'a ne bayan ya shafe kwanaki hudu a hannun 'yan bindigar da suka dauke shi a kamfaninsa dake rukunin masan'antu na Sharada a birnin na Kano.

Babu tabbas ko an biya kudin fansa kafin sakinsa.

Shugaban kungiyar 'yan Lebanon mazauna Kano Tahir Fadlallah ya tabbatar wa BBC sakin Hasan din, inda yace yana cikin koshin lafiya, sai dai yaki cewa komai kan ko an bada fansa gabanin sakinsa.

Karin bayani