Bom ya kashe mutane biyar a Lebanon

Image caption Jami'an tsoro na duba motar da ta fashe da bom a Beirut

Wani kakkarfan bom da ya tashi a Beirut, babban birnin Lebanon ya kashe Muhammad Chatah, tsohon ministan kudi mai goyon bayan 'yan tawayen Syria.

Kamfanin dillancin labaran Lebanon ya ce bom din ya kashe wasu mutanen hudu tare da jikkata fiye da mutane 50.

Mr Chatah, Musulmi dan Sunni, mashawarcin tsohon Pirai minista Saad al-Hariri ne, wanda jagoran masu adawa da shugaban Syria Bashar al-Assad ne dake samun goyon bayan kasashen Yamma.

A sanarwar da ya fitar, Mr Hariri ya zargi kungiyar Hezbollah da kai harin, kodayake bai ambaci sunan kungiyar 'yan bindigar ta 'yan Shia ba wacce 'yar gani-kashenin shugaba Assad ce.

Lebanon na fama da hare-haren bama-bamai cikin watannin da suka gabata sanadiyyar sabanin akida game da rikicin Syria mai makwabtaka.

Karin bayani